1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin manoya ya barke a Chadi

Abdul-raheem Hassan MAB
August 31, 2020

Akalla mutane 10 sun mutu a wani sabon rikici da ya kunno kai tsakanin manoma da makiyaya a kudancin kasar Chadi, rikicin da ya barke bayan da makiyaya suka gano shanunsu a wata gona. 

Leben am Tschadsee in Afrika
Hoto: picture-alliance/dpa

A cewar wani jami'in gwamnati mai kula da harkokin shari'a a Moundou babban birnin lardin kudancin Chadi, an samu asarar rayuka mutane lokacin da manoma suka kai harin daukar fansa a wurin da makiyaya suke jan'izar dan uwansu.

Hukumomi sun tsare mutane 43 da ake zargi da hannu a sabon rikicin ciki har da mai garin wani kauye. An sha samun tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya da shigowa daga Sudan suna bin burtali ta gonaki, lamarin da ke tayar da hankalin manoma idan shanu sun musu barna.