1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 10 sun mutu a wani hari a Mogadishu

Mouhamadou Awal Balarabe
March 1, 2019

Mayakan al Shabaab sun dauki alhakin halaka mutane da dama a harin da suka kai a birnin Mogadishu na Somaliya. Hukumomi suka ce adadin wadanda abin ya shafa zai iya karuwa.

Schwere Explosion in Mogadischu
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/F. A. Warsameh

Akalla mutane goma sun rasa rayukansu a Mogadishu na Somaliya lokacin da wata mota makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da wani kasaitaccen otal da ke tsakiyar birnin. Sannan rahotannin sun bayyana cewa wani mai fafutuka da makamai na musayar wuta da dakarun gwamnatin kasar ta Somaliya a yanzu haka. 
A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan ranar Jumma'a, kungiyar al Shabaab ta yi ikirarin kaddamar da hare-haren a kan jami'an tsaro.  Sai dai hukumomi sun bayyana cewar adadin wadanda suka rasu na iya karuwa, saboda ana ci gaba da tono gawarwakin da ke binne a baraguzan ginin otal din na al-Mukarama. 
Duk da cewa an kori 'yan al shabaab daga Mogadishu a shekara ta 2011, amma har yanzu wasu yankuna na karkarar Somaliya na karkashin ikonsu. Kuma sun sha alwashin ganin bayan gwamnatin Somaliya wacce ke samun goyon bayan kasashen duniya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW