Mutane 10 sun rasu a Maiduguri sakamakon fashewar bam da harbr harbe
December 13, 2011Aƙalla mutane 10 majiyoyin asibiti suka ce sun rigamu gidan gaskiya sannan wasu 30 sun jikata a fashewar wani bam tare da musayar wuta da suka auku a birnin Maiduguri mai fama da tashe tashen hankula dake jihar Borno ta arewa maso gabacin tarayyar Najeriya. Wata ma'aikaciyar jiya da ta ƙi a baiyana sunanta, ta faɗawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa an kai musu gawarwaki 10 da kuma mutane 30 da suka sami rauni wasu rauni mai tsanani a asibitin. Nas ɗin ta ce bisa munin raunin da wasu suka ji, musamman na harbi bindiga, to yawan waɗanda za su mutun zai ƙaru. Mazauna garin na Maiduguri sun zargi sojoji da harbi irin na kan mai uwa da wabi da ƙone gidaje biyo bayan harin bam ɗin da aka kai kan dakarun. Sai dai rundunar soji ta musanta zargin.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman