1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Maharin Sweden na cikin wadanda suka mutu

Suleiman Babayo AH
February 5, 2025

Mutane 11 suka mutu ciki har da maharin sakamakon harbin da aka yi a wata cibiyar ilimin manya da ke Sweden inda 'yan sanda ke ci gaba da gudanar da bincike domin sanin dalilin haka.

Cibiyar ilimi da aka kai hari a Sweden
Cibiyar ilimi da aka kai hari a SwedenHoto: Kicki Nilsson/TT News Agency/AP Photo/picture alliance

A kasar Sweden zuwa yanzu mutane 11 aka tabbatar sun halaka sakamakon harbin da aka yi a wata cibiyar ilimin manya da suka hada da dan bindigar, sannan akwai wasu mutane biyar da suka tsira da munanan raunika.

Karin Bayani: An kashe Salwan Momika wanda ya kona al Qur'ani a Sweden

'Yan sanda suna ci gaba da gudanar da bincike, domin sanin dalilan da suka janyo dan bindiga dadin ya bude wuta wa mutane kuma daga bisani ya kashe kansa. Firaminista Ulf Kristersson na kasar ta Sweden ya ce wannan shi ne kisa mafi mutane da hanyar harbe mutane da kasar ta fuskanta, amma ya yi alkawarin binciken sanin dalili domin magance na gaba.