1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iPakistan

Iftila'in ambaliyar ruwa ya halaka 143 a Pakistan

Suleiman Babayo USU
April 30, 2024

A kasar Pakistan ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa sun halaka mutane 143 tare da lalata gidaje da amfanin gona cikin watan Afrilu mai karewa kuma akwai yuwuwar lamarin zai tabarbare cikin watanni da suke tafe.

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Ambaliyar ruwa a PakistanHoto: Hussain Ali/Zuma/IMAGO

Ambaliyar ruwa da zabtarewar kasar gami da tsawa da aka samu sakamakon ruwan sama da aka tafka a kasar Pakistan sun halaka mutane 143 cikin wannan wata na Afrilu. Sannan hukumomi sun ce ambaliyar ta kuma lalata gidaje masu yawa gami da lalata amfanin gona.

Hukumar kula da sararin samaniya ta Pakistan ta ce akwai yuwuwar lamura za su kara sukurkucewa zuwa watan Yuli, inda ake sa ran samun karin ruwa sama mai karfi.