Mutane 15 za su yi takara a Nijar
January 9, 2016Talla
Kotun kundin tsarin mulki a jamuhuriyar Nijar, ya yasanar da cewa fitaccen dan adawan kasar Malam Hama Amadou na da cikin jerin wandanda za su yi takaran shugaban kasa a zaben kasar da ke tafe. Kotun a hukuncin da ta yanke yau Asabar 10.01.2015, ta amince da takaran shugaban kasa ga mutane 15, a ciki harda Hama Amadou wanda ya kwashe lokaci yana hijira wejen kasar. A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, amincewar da kotu ta yi ga takaran Hama Amadou zai zama kalubale da mastin lamba kan gwamnatin Nijar, ta sako Hama wanda hukumomi suka daure shi tun bayan komar warsa gida. Yanzu dai bisa hukucin da kotun ta yi, mutane 15 kenan za su yi takaran shugabancin jamhuriyar Nijar a zaben ranar 21 gawatan gobe.