Kungiyar IS ta dauki alhakin harin Afghanistan
November 2, 2020Talla
Bayan kwashe sa'oi ba a san wadanda suka kai harin ba, amma daga bisani Kungiyar IS ta dauki alhakin kai farmaki. Dama can kungiyar Taliban ta baiyana cewa ba tada hannu a harin.
Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan Afghanistan din Tariq Arian ya ce 3 daga cikin maharan sun hallaka yayin farmaki, tuni dai dakarun wanzan da zaman lafiya suka killace harabar makarantar domin tabbatar da cikakken tsaro.