Mutane 24 suka rasu a zanga-zangar Burkina Faso
November 26, 2014Masu zanga-zangar da suka fusata da tsawon wa'adin mulkin Blaise Compaore da ya nemi a kara masa wa'adin mulki bayan kusan shekaru 30 yana dare bisa kan mulki sun sanya wuta a majalisar dokokin kasar da ma tilastawa tsohon shugaban sauka daga kujerar sa a ranar 31 ga watan Oktoba da ta gabata.
Clarisse Ouoba, da ta jagoranci kwamitin ta bayyana wa manema labarai cewa mutane 24 ne suka rasu a lokacin zanga-zangar a yayin da wasu sama da dari shida suka samu raunika sannan an afkawa gidajen wasu ministoci da 'yan majalisa inda aka yi musu sace-sace. ko da ya ke tun da fari 'yan adawa sun ce mutane talatin ne suka rasu a rikicin.
Yanzu dai gwamnatin rikon kwarya ke jan ragamar mulkin wannan kasa da ke a yammacin Afrika a inda ake saran gudanar da zabe a shekara me zuwa.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu