1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 28 sun mutu sanadiyyar hari a Libiya

June 9, 2013

Kimanin mutane 60 ne suka sami rauni baya ga wadanda su ka mutu sakamakon hari a Benghazi na Libiya.

Protesters run for cover during an attack on a Libyan militia, the Libya Shield brigade, headquarters in Benghazi, June 8, 2013. At least 11 people were killed and 35 wounded in clashes on Saturday between protesters and a Libyan militia operating with Defence Ministry approval in the eastern city of Benghazi, a doctor in the city said. Residents said dozens of protesters had demonstrated outside the headquarters of the Libya Shield brigade demanding the disbanding of militias who have yet to lay down their weapons nearly two years after the overthrow of long-time dictator Muammar Gaddafi. REUTERS/Esam Al-Fetori (LIBYA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) (eingestellt: qu)
Hoto: Reuters

Kimanin mutane 28 ne su ka riga mu gidan gaskiya lokacin da aka yi wata arangama a shelkwatar tsoffin 'yan tawayen da su ka hambarar da gwamnatin marigayi Mou'ammar Ghaddafi na Libiya.

Jami'an asibiti a birnin Benghazi inda nan ne aka kai harin sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar baya ga wadanda su ka rasu, wasu karin mutane 60 sun sami raunuka wasu daga cikinsu ma munanan.

Arangamar dai da ma abubuwan da su ka biyo baya sun samo asalin ne lokacin da wani gungun masu zanga-zanga suka afkawa tsoffin 'yan tawayen na Libya inda su ka yi kokarin fidda su daga shelkwatar ta su da nufin mamaye wajen, batun da ya jawo dauki ba dadi.

Da ya ke tsokaci kan harin Adel Tarhuni da ke zaman mai magana da yawun tsoffin 'yan tawayen na Libiya wanda ake wa lakabi da Sheild of Libya, ya ce mambansu guda ya rasu yayin da wasu su ka jikkata.

Tuni dai gwamnatin ta Libya ta yi Allah wadai da wannan harin inda kakakin rundunar sojin kasar Kanar Ali al-Shikhi ya ce harin tamkar afkawa gwamnatin kasar ce domin tsoffin 'yan tawayen wani bangare ne a sojin kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Ahmed Salisu