Harin ta'adanci ya hallaka mutane 29 a Iran
September 22, 2018Shugaba Hassan Rohani na Iran ya sha alwashin mayar da martani mai tsanani bayan harin ta'addancin da wasu mutane dauke da makammai suka kai yayin wani faraitin sojoji wanda kuma ya janyo mutuwar mutane 29 cikinsu har da fararan hula.
Harin da hukumomin na Teheren suka kira shi da na ta'addanci ya wakana ne a birnin Ahwaz da ke a matsayin babban birnin jihar Khuzestan a Kudancin kasar, jihar da ke da tarin jama'a akasarinsu Larabawa, kuma harin ya kasance hari mafi muni da kasar bata fuskanshi irinsa ba yau kusan shekaru takwas.
Wasu mutane 57 sun samu raunuka wanda da dama daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali sakamkon wannan hari, wanda ya wakana a jajibirin bulaguron da shugaban na Iran Rouhani zai yi zuwa Amirka, domin halartar babban zaman taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara, taron da zai gudana a lokacin da ake samun tashin jijiyoyin wuya tsakanin Amirka da kasar ta Iran.