Mutane 31 sun rasu a wani hari a China
May 22, 2014Talla
Gidan talabijin din China na CCTV ya ce an jefa abubuwan fashewar ne cikin kasuwar daga cikin wasu motoci, yayin guda daga cikin motocin da ke makare da abubuwan na fashewa ta tarwatse.
Tuni dai baban jami'in tsaron kasar da ke yankin da abin ya faru ya danganta harin a matsayin na ta'addanci, yayin da kamfanin dillancin labarai na China na Xinhua ya rawaito shugaban kasar na cewar gwamnati za ta hukunta wanda aka samu da hannu wajen kai harin kuma ta lashi takobin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
A baya dai gwamnatin China ta sha danganta tada kayar bayan da ake samu a yankin da harin na yau ya wakana da 'yan awaren da ke Xinjiang din.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman