1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Mutane 40 sun mutu a wani hari a Nijar

March 22, 2021

Rahotanni daga jihar Tahoua ta Nijar na nuna cewa sama da mutane 40 ne suka rasa rayukansu a wani harin ta'addanci da aka kai wasu kauyuka da ke kan iyakar Jamhuriyar Nijar da kasar Mali.

Symbolbild Niger Soldat
Hoto: Ludovic Marin/AFP/Getty Images

Jami'an tsaro a yankin Tahoua sun ce wasu a kan babura da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari kauyuka uku da ke yankin a ranar Lahadi. Ko a ranar 15 ga watan Maris din shekarar 2021 ma mutane 66 sun rasa rayukansu a yankin da ke zama iyakar kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali, yankin da ya yi kaurin suna wajen kai hare-haren ta'addaci.