Mutane 40 sun mutu a Mali
April 29, 2018Talla
Hukumomi a kasar Mali, sun ce akalla mutane 40 sun mutu cikin makonni biyun da suka gabata, a kashe-kashen da 'yan bindiga masu kaifin kishin addini suka kaddamar a kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar. Gwamnan yankin Menaka Daouda Maiga, ya ce a ranakun Alhamis da Juma'a da suka gabata ma sai da wasu 'yan bindiga bisa babura suka buda wuta kan jama'a.
Ya kuma yi zargin wasu makiyaya da ke alaka da kungiyar IS a yankin da kaddamar da hare-haren a matsayin ramuwar gayya kan sojojin yankin. Ana dai ganin karin hare-hare a tsakanin kasashen na Mali da Nijar a 'yan tsakanin nan a yankin arewa maso gabashin kasar. Hare-haren dai na iya zama wani yunkuri ne na ta'azzara lamura tsakanin Fulani da kabilun yankin, kan ikon mallakar filaye.