1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaduwar cuta mai toshe numfashi a China

Abdullahi Tanko Bala
January 22, 2020

Kungiyar lafiya ta duniya na nazarin ayyana yaduwar kwayar cutar coronavirus mai toshe hanyoyin numfashi a matsayin wadda ke bukatar kulawar gaggawa a duniya baki daya bayan da mutane 440 suka kamu da cutar

China Corona-Virus in Wuhan
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Dake Kang

Hukumomi a China sun ce an sami karin yaduwar cutar coronavirus mai nasaba da toshewar hanyoyin numfashi inda kawo yanzu mutane 440 suka kamu da ita yayin da yawan wadanda suka rasu a sakamakon kwayar cutar ya kai mutum tara a wannan Laraba.

Mukaddashin daraktan hukumar lafiya ta kasar Li Bin ya shaidawa manema labarai cewa dukkan mace macen sun auku ne a birnin Wuhan da ke gundumar Hubei.

Sabbin alkaluman mace macen na zuwa ne kasa da kwana guda bayan da aka rahoton wani da ya kamu da cutar a Amirka.

Hukumar lafiyar ta sanar da hanyoyin kare yaduwar cutar yayin da miliyoyin jama'a ke zirga zirgar tafiye tafiye a wannan makon saboda hutun sabuwar shekara ta China. Matakan sun hada da feshin magani a filayen jiragen sama da tashoshin jiragen kasa da manyan shagunan kasuwanci.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW