1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciNajeriya

Mutane 6 sun mutu bayan fashewar bam kirar gargajiya a Borno

Mouhamadou Awal Balarabe
January 28, 2024

Wani jami'i ya ce bam ya fashe yayin da wasu mutane biyu ke dibar karafa a cikin dajin da ke kusa da garin Gubio mai tazarar kilomita 80 da Maiduguri babban birnin yankin, lamarin da ya salwantar da rayuka.

Taswirar Najeriya
Taswirar Najeriya

Mutune shida da suka hada da kananan yara hudu sun riga mu gidan gaskiya a lokacin da wani bam kirar gargajiya da aka dasa a cikin daji ya tashi a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya. Wani jami'in yankin ya ce bam din ya fashe ne a ranar Asabar, yayin da wasu mutane biyu ke dibar karafa a cikin daji da ke kusa da garin Gubio mai tazarar kilomita 80 da Maiduguri babban birnin yankin.

Kimanin mutane 40,000 ne aka kashe tare da raba miliyan biyu da muhallansu tun bayan barkewar matsalar tsaro a yankin Arewa maso gabashin Najeriya shekaru 14 da suka gabata. Galibin 'yan yankin da suka rasa matsugunansu na zama ne a sansanonin wucin gadi, inda suke shiga daji don neman itace da tarkacen karafan motocin, da nufin sayarwa don samun abinci. sai dai masu gagwarmaya da makamai na kai musu hari daga sa'i zuwa lokaci bisa zarginsu da yin leken asiri ga dakarun tsaro.

A watan Yunin 2023, hukumomi a Borno sun hana kwasar karafa a daji saboda dalilai na rashin tsaro, ba tare da ta ga tasirin matakin ba. Ko watannin da suka gabata, sai da mutane 13 da suke neman karafa suka mutu, wasu uku kuma suka jikkata a lokacin da wani abin fashewa ya tarwatse a garin Bama, kusa da wani dajin da ake dauka a matsayin tungar masu ikirarin jihadi.