1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 83 sun mutu a gobarar Hong Kong

Abdullahi Tanko Bala
November 27, 2025

Hukumomin Hong Kong sun ce mutanen da suka mutu a gobara mafi muni da ta auku a birnin sun kai akalla mutane 83 yayin da ma'ikatan kwana-kwana ke ci gaba da neman mutane 250 da suka bace.

Rukunin gidaje da gobara ta kama a Hong Kong
Rukunin gidaje da gobara ta kama a Hong KongHoto: Peter Parks/AFP

Hukumomin Hong Kong sun ce mutanen da suka mutu a gobara mafi muni da ta auku a birnin sun kai akalla mutane 83 yayin da ma'ikatan kwana-kwana ke ci gaba da neman mutane 250 da suka bace.

Har yanzu hayaki na tashi a dogayen benaye takwas na rukunin gidajen da gobarar ta auku.

Hukumomin sun ce an kaddamar da bincike kan musabbabin aukuwar gobarar mafi muni da ba a taba ganin irinta ba cikin shekaru 80 a birnin kasuwancin inda suka ce suna binciken gyaran da ake yi a gidajen inda aka bar wasu abubuwa kamar ledoji da shingen roba a wurin wadanda ke iya kamawa da wuta.

Yan sanda sun ce sun kama mutane uku bisa zargin sakaci na barin abubuwan da ke iya kamawa da wuta a wurin da gobarar ta tashi.