Mutane biyar sun hallaka cikin hari a Sudan
October 9, 2012
Talla
Mutane biyar sun hallaka yayin da wasu 20 su ka samu raunuka, lokacin da 'yan tawaye su ka kai hari a Jihar kudancinKordofan ta Sudan.
Gidan rediyon gwamnati ya bayyana cewa an kai harin jiya Litinin, tare da zargin ƙungiyar SPLM ta arewaci ka kaiwa. Amma ƙungiyar ta ce babu farar hula da harin ya shafa. Ita ma gwamnati ba ta fayyace wadanda harin ya ritsa da su ba.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammadou Awal Balarabe