Mutane biyu sun rasu a zanga-zangar Masar
November 28, 2014Akalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon wata arangama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a kasar Masar, yayin da magoya bayan tsofon shugaban kasar Mohamed Morsi da sojojin kasar suka hembare a watan Yuli na 2013 suka fito domin kalubanantar hukumomin kasar. A kalla dai an kama mutane fiye da 200 daga cikin masu zanga-zangar.
Kungiyar 'yan Salafiyya ce dai ta kasar mai goyon bayan tsofon shugaba Morsi ne ta kira wannan zanga-zangar bayan sallar Juma'a da zimmar neman kifar da gwamnatin shugaba Abdel Fatah Al-sissi wadda tuni aka tura jami'an tsaro suka tarwatsa su. Da ma dai hukumomin na masar sun dauki kwararan matakkai kan wannan lamari inda suka zuba sojoji da 'yan sanda a Alkahira babban birnin kasar, da kuma sauran manyan biranen kasar. A cikin unguwar Matariya ce dai da ke gabashin birnin na Alkahira aka samu arangamar da tayi sanadiyyar mutuwar mutanen biyu.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal