Mutane da dama sun mutu a Maiduguri
October 16, 2015Talla
Wasu shaidun gani da ido sun ce 'yan kunar bakin wake ne su biyu da suka shigo masallacin cikin tufafi na musulmi inda daya ya fara tayar da bam din da ke a jikinsa kafin na biyu shima ya tayar da nashi a daidai lokacin da jama'a ke kokarin bada agaji ga wadanda harin farkon ya rutsa da su a dai dai lokacin da ake shirin sallar magariba .Wani shima da ke kusa da masallacin lokacin abkuwar lamarin ya ce ya kirga gawarwaki 42 na mutanen da suka halaka a cikin harin.
Hukumomin 'yan sanda na birnin na Maiduguri sun tabbatar da kai harin sai dai sun ce mutane 14 ne suka mutu a cikin. Tashin bam din ya ruguza ginin masallacin wanda ya taushe tarin masallata inda da dama daga cikinsu suka ji raunuka.