Mutane da dama sun mutu a Somaliya
July 31, 2017Talla
Akalla mutane 25 ne jami'ai suka tabbatar da salwantarsu a Somaliya bayan wata arangama tsakanin mayakan Al Shabaab da dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka ta AU. Lamarin dai ya faru ne a yankin Shabelle kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Mayakan Al Shabaab, sun yi ikirarin halaka dakarun na AU 39 a kwanton baunar da suka yi wa sojojin, sai dai har ya zuwa yanzu ba su tabbatar da sahihancin ikirarin ba. Rahotanni sun ce mayakan na tawaye na tsananta hare-hare kan dakarun na kasashen na Afirka.
Kimanin dakaru dubu 20 ne dai kungiyar ta AU ta girke a Somaliyar musamman saboda fuskantar 'yan jihadin na Al Shabaab.