Bam ya halaka mutane da dama a Maiduguri
June 22, 2015Talla
Akalla mutane 30 sun rasu sannan da dama sun samu raunuka a wani harin kunar bakin wake da wasu 'yan mata biyu suka kai kusa da wani masallaci cike da masu ibada da ke a wata tashar mota a Maiduguri. Harin da kuma ya auku kusa da kasuwar kifi da ke hanyar Baga Road shi ne irinsa na hudu da aka kai a Maiduguri a cikin wannan wata. Wani da ya shaida abin da ya faru ya ce yarinya daya ta tayar da bam din ne lokacin da ta tinkari masallacin lokacin sallar La'asar. Dayar kuma da alama tana gudu sai ta tarwatsa bam din da take dauke shi, ta kashe kanta da kanta. Ana dai zargin kungiyar Boko Haram da kai irin wadannan hare-hare.