SiyasaAfirka
Mutane da dama sun mutu a wani sabon rikici a Chadi
May 15, 2025
Talla
Gwamnatin Chadi ta sanar da cewa wani sabon rikici ya halaka mutane akalla 35, duk da cewa hukumomin N'Djamena basu yi cikakken bayani dangane da rikicin ba.
Karin bayani:Ambaliya: Kwalara ta barke a Kamaru da Chadi
Ministan Yada Labarai kuma kakakin gwamnati Gassim Cherif Mahamat ya kara da cewa mutane shida sun jikkata a yayin rikicin da ya afku a lardin Logone-Occidental. Ministan ya kara da cewa tuni jami'an tsaro suka shawo kan rikicin.