Mutane da dama sun mutu sakamakon harin 'yan bindiga a Neja
March 22, 2024Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 21 a jihar Neja da ke yankin Arewa maso yammacin Najeriya, a wani hari da aka kai a wata kasuwa mai cunkoson jama'a. Wannan harin ya biyo bayan garkuwa da jama'a da aka yi a wannan wata da kuma sace tarin ‘yan makaranta a jihar Kaduna.
Karin bayani: Dabi'ar sace-sacen mutane na kara kamari a Najeriya
Wani basarake Alhaji Isah Bawale da kuma al’ummar karkarar Madaka sun bayyana wa kanfanin dillancin labaran Reuters cewar ‘yan bindiga sun shiga kasuwar a ranar Alhamis tare da bude wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. Sannan sun kara da cewa hukumomi na ci gaba da tattara bayanai game da wadanda suka mutu da wadanda suka bace.
Karin bayani: Rashin tsaro na mummunan tasiri kan noma a jihar Filato
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja Bello Abdullahi Mohammed ya tabbatar da harin, amma bai bayar da cikakkun bayanai. Satar mutane don neman kudin fansane neman zama ruwan dare a arewacin Najeriya.