1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun mutu, wasu sun jikata sakamakon hargitsi akan iyakokin Isra'ila

May 15, 2011

Dubun dubatan Falasɗinawa sun fito kan tituna don yin zanga-zangar ƙin lamirin Isra'ila a ranar Nakba ta tunawa da korarsu bayan kafa Isra'ila a 1948.

Hoto: picture-alliance/dpa

Tashe tashen hankula da suka auku akan iyakokin Isa'ila sun dabaibaye ranar da Falasɗinawa ke tunawa da korarsu daga yankunansu na asali. Rahotanni sun ce sojojin Isra'ila su harbe Falasɗinawa 10 har lahira akan tuddan Golan lokacin da suka kutsa kan iyakar mai cikkaken tsaro daga Siriya. Wannan dai shi ne wani lamari mafi muni da ya auku cikin shekaru da dama. Siriya ta yi tir da matakan da Isra'ila ta ɗauka da cewa laifi ne. A kuma kan iyakar Isra'ilar da Libanon an harbe masu zanga-zanga 10 har lahira lokacin da suke jifar sojojin Isra'ila da duwatsu. Mutane da dama suka jikata a lamuran guda biyu. A ma can kan iyakar Eres da Zirin Gaza sojojin na Yahudun Isra'ila sun jiwa Falasɗinawa kimanin 70 raunuka sakamakon harbin da suka yi musu. A garuruwan Hebron na yammacin Kogin Jordan da kuma gabacin Birnin Ƙudus an yi taho mu gama. A rana irin ta yau da ake kira Nakba wato bala'i, dubun dubatan Falasɗinawa sun fito kan tituna don yin zanga-zangar ƙin lamirin Isra'ila. A yau Falasɗinawa ke tunawa da fatattakan Larabawa da aka yi bayan kafa ƙasar Isra'ila a watan mayun shekarar 1948.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman