1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Cututtuka na iya halaka mutane fiye da harin bam a Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
November 28, 2023

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mutane da yawa na iya mutuwa daga cututtuka fiye da na tashin bama-bamai a cikin Gaza idan ba a gyara sashin kula da lafiyar al'umma ba.

Hoto: Montaser Alswaf/Anadolu/picture alliance

Hukumomin kiwon lafiya na Gaza wanda MDD ta aminta da su, sun ce an tabbatar da kashe mutane fiye da 15,000 a hare-haren da Isra'ila ke kaiwaGazakusan kashi 40 cikin 100  kananan yara, daura da wasu dubbai da ake fargabar sun mutu kuma ke karkashin baraguzan gine gine.

Isra'ila ta lashi takobin kakkabe kungiyar Hamas da ke mulkin Zirin Gaza, bayan da 'yan bindiganta suka yi nasarar tsallaka shingen da ya raba- yankunan, a hari mafi muni a kan Isra'ila, da ya kashe mutane kusan 1,200 tare da kama wasu 240 tun a ranar 7 ga Oktoba.

A yayin da aka shiga rana ta biyar natsagaita wutarwucin gadi don shigar da kayan jin kai da musayar fursunoni da wadanda aka yi garkuwa da su, dakarun Isra'ilan na ci gaba da kai somame ta kasa ungunnin gabar yamma da kogin Jordan, inda aka kashe wani yaro da kama matasa da yawa.