Mutane fiye da 120 ne suka mutu a hare-haren bama-bamai a Kano
January 21, 2012A Jihar Kano da ke arewacin Tarayyar Najeriya, an tabbatar da mutuwar mutane fiye da 120 a jerin hare-haren bama-bamai da aka kai a cikin birni, inda ake ci gaba da ganin gawawwaki akan tituna. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani kakakin ƙungiyar Boko haram ya ɗauki alhakin waɗannan tagawayen hare-haren da aka ƙaddamar a gidan wani babban jami'in 'yan sanda, da ofishin shige da fice na jihar ta kano da kuma hekwatar 'yan sanda ta jihar.
Gwamnan Jihar Rabi'u Musa kwankwaso ya kafa dokar hana fita na sa'o'i 24. Kana ana ci gaba da ɗaukar ƙwararan matakan tsaro bayan hare-haren bama-bamai da aka kai a wurare daban daban na birnin na kano.wakilin Deutsche Welle a Kano ya nunar da cewa harkoki sun tsaya cik a birnin da ke arewacin Najeriya da ya yi fice a harkokin saye da sayarwa.
A birnin Yenagoa da ke kudancin Najeriya ma dai an sami fashewar wasu abubuwa guda biyu masu ƙarfi sai dai hukumomin jihar ta Bayelsa da ke zama mahaifar shugaban ƙasar Goodluck Jonathan sun ce babu wanda ya sami rauni a harin.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala