SiyasaAmurka
New Orleans: Wata babbar mota ta yi kutse a cikin jama'a
January 1, 2025
Talla
Wani rukunin kamfanonin sadarwa na CBS ya bayar da rahoton cewar, wata babbar mota ta shiga cikin jama'a a tsiyace, kafin matukinta ya yi tsalle ya fara yin harbin bindiga, abin da ya sa ‘yan sanda suka mayar da martani. Wannan lamari da ya auku dab da lokacin da ake gudanar da bukuwan sabuwar shekara har yanzu ba a tantance dalilansa ba sannan babu wani karin bayyani a kai yazuwa yanzu.