1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Mutane miliyan 100 sun rasa matsugansu

May 23, 2022

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin Ukraine da sauran rikice-rikice sun tilastawa kimanin mutane miliyan dari a duniya rasa matsugunnansu.

Konflikt in Äthiopien - Flüchtlinge im Sudan Tigray
Hoto: Marwan Ali/picture alliance/dpa

Hukumar ta ce wannan adadi abun tayar da hankali ne kasancewar wannan ne karon farko da aka taba samun alkaluma mai yawa a tarihi.

Alkalumman hukumar a bara sun yi nuni da cewa kimanin mutane miliyan 90 ne suka rasa matsagunnansu biyo bayan rikice-rikice a kasashen Habasha da Burkina Faso da Myanmar da Najeriya da Afghanistan da kuma Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango. 

Mamayar da Rasha ta kaddamar a kasar Ukraine a watan Fabarairun wannan shekarar kuma ya haifar wa mutane fiye da milyan takwas rasa matsugansu yayin da wasu kimanin miliyan shida suke gudu daga kasar kwata-kwata.