1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar karancin abinci ga jama'a a yammacin Afirka

Usman Shehu Usman
April 21, 2020

Akalla mutane miliyan 50 ne ka iya fuskantar barazanar fadawa ckin yunwa da karancin abinci a yankin yammacin Afirka sakamakon yaduwar cutar Coronavirus da matsalar fari da tsaro.

eco@africa Mali erneuerbare Energien
Hoto: DW

Annboar coronavirus da matsalar fari da tabarbarewar tsaro da ke ci gaba addabar yankin Afirka ta Yamma na haddasa barazanar yunwa ga mutun miliyan 50 kamar yadda wani bincike da kungiyar agaji Oxfam ta bayyana.

Kungiyar ta ce za a samu adadin ne a cikin watan Augusta inda zai zarta na mutun miliyan 17 da aka yi hasashe kyautata zaton za su fuskanci karancin abinci a cikin watan Yuni.

Binciken ya ce duk da matakan da gwamnatocin kasashen da ke yammacin Afirka ke ci gaba da dauka, al'ummomin kasashen musamman ma a karkara na fama da matsaloli na samun kayayakin abinci bisa matakan dokokin kulle da hukumomi ke dauka da rufe iyakokin kasashen baya ga rashin tabbatacen tsaro da wasu kasashen ke fama da shi inji kungiyar.