Rashin aikin yi na karuwa a duniya
January 21, 2020Talla
Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar tare da tallafin kungiyar kwadago ta duniya ILO yace mutane kimanin miliyan 500 a fadin duniya basu da aiki nagartacce ko kuma basu ma da aikin yi.
Rahoton yace an sami dan daidaiton rashin aiki a shekarar 2010 sai dai kuma ana kyautata tsammanin rashin aiki zai karu zuwa mutane miliyan biyu da rabi a wannan shekarar ta 2020.
Shugaban kungiyar kwadago ta duniya Guy Ryder yace miliyoyin ma'aikata a duniya suna rayuwa hannu baka hannu kwarya. Adadin marasa aikin su miliyan 470 a fadin duniya daidai yake da kwatankwacin kashi 13 cikin dari na daukacin ma'aikata a duniya baki daya.