Mutane sama da 100 sun samu raunuka a Switzerland
January 1, 2026
Baturen 'yan sandan yankin ya sanarwa da manema labarai cewa har ya zuwa wannan lokaci suna ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar, a daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da shagulgulan shiga sabuwar shekara. Hukumomin Switzerland sun tura jiragen helikwafta da motocin kashe gobara zuwa yankin da ake gudanar da wasan dusar kankara.
Karin bayani:Gobara ta hallaka mutane 232 a Brazil
Gwamnan Lardin Montana, Mathias Rénard, ya ce asibitin da ke yankin ya cika makil, sakamakon marasa lafiyan da ke bukatar agajin gaggawa. A sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta Shugaban Switzerland, Guy Parmelin ya aike da sakon ta'aziyya ga 'yan uwa da abokan arzikin wadanda suka rasa rayukansu, tare da kuma da addu'ar waraka ga wadanda suka jikkata.