Mutane sama da 70 sun mutu a harin Taliban
October 17, 2017Talla
Mataimakin ministan cikin gida na kasar Janar Murad Ali Murad ya ce mutane 41 da suka hada da fararan hula 20 suka mutu a yayin da wasu 160 da suka hada da fararan hula 110 suka jikkataa harin da aka kai a wani ofishin 'yan sanda na garin Gardez na jihar paktiya ta Kudu maso Gabashin kasar.
Harin na biyu a kai shi ne kusan a lokaci daya a birnin Andar na jihar Ghazni inda jami'an tsaro 25 da fararan hula biyar suka halaka. Wani kakakin Kungiyar Taliban ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa kungiyarsu ce ke da alhakin kai wannan hari, wanda ya ce sun kai shi ne a matsayin martani ga jerin hare-haren da Amirka ta kaddamar a baya bayan nan da jirage maras matuka na Dron.