1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Mutane sun fice daga yankunan arewacin Isra'ila

Musa Tijjani Ahmad Emily Gordine/SB
October 23, 2024

Yankunan arewacin Isra'ila da ke kan iyaka da kasar Lebanon sun zama kufai sakamakon ficewar dubun dubatar mutane saboda hare-haren rokoki da makamai masu linzami daga mayakan kungiyar Hezbollah.

Iyakar Isra'ila da Lebanon
Iyakar Isra'ila da LebanonHoto: Israel Defense Forces/Handout/Xinhua/picture alliance

Yankunan arewacin Isra'ila da ke kan iyaka da kasar Lebanon sun zama kufai sakamakon ficewar dubun dubatar mutane domin hare-haren rokoki da makamai masu linzami daga mayakan Hezbollah, a yakin da Isra'ilan ke ci gaba da gwabzawa da mayakan. Guda daga cikin manyan biranen yankunan arewacin Isra'ila shi ne Kiryat Shmona da a halin yanzu mutane kalilan ne ke rayuwa a birnin.

Karin Bayani: Yara na kwana a kan titunan Beirut sakamakon rikici

Iyakar Isra'ila da LebanonHoto: Avi Ohayon/REUTERS

Kowa ya cika wandonsa da iska a yankunan da ke kan iyakar kasashen biyu da ke ci gaba da luguden wuta a tsakaninsu. Rahotannin da ke fitowa daga yankin arewacin Isra'ilan na cewa daga cikin garuruwa akalla 32 da ke da nisan mile 82 kwatankwacin kilomita 212 da ke kan iyakar Lebanon da lardin Mater Asher na Isra'ila sun zama kufai, kai har ma da wasu kauyukan Larabawa guda biyu da ke yankin babu kowa a ciki.

Haka lamarin yake a birnin Kiryat Shmona da al'ummar yankin suka nemi tudun muntsira a wasu sassan Isra'ila, in ban da mutane kalilan irin su Sergio Helman da ke sana'ar dafa abinci kuma ya zabi zama a yankin duk wuya ko dadi musamman ga sojojin Isra'ila da ke kai komo a yankin kadomin ba da taimakon da ya dace.

Iyakar Isra'ila da LebanonHoto: Jalaa Marey/AFP/Getty Images

Shi dai Sergio Helman na daya daga cikin mazauna arewacin Isra'ila da ke dab da iyakar Lebanon da ya yanke shawarar zama a yankin duk da barazanar da ake fuskanta na hare-haren Hezbollah, kasancewar a kullum babu abin da kake ji in ban da karar rokoki da makamai masu linzami da jirage marasa matuka daga Hezbollah. Ko a kwanakin da suka gabata hare-haren mayakan na Hezbollah sun halaka wasu fararen hula biyu.

Ana hasashen cewa ko da an kammala yakin Isra'ila da Hezbollah; rabin al'ummar Kiryat Shmona ba za su dawo yankin ba, saboda hukumomin Isra'ila sun gaza ba su cikakken tsaro gabanin farmakin mayakan na Hezbollah. Babban ayar tambayar ita ce, shin sojojin Isra'ila za su bai wa al'ummar yankin arewacin kasar tabbacin tsaro idan sun koma gida.