1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sun mutu a gangamin Kamfe ɗin shugaba Jonathan

February 12, 2011

An tattake mutane har lahira sakamakon turmutsitsi a lokacin kamfe ɗin shugaba Goodluck Jonathan a garin Fatakwal ta Jihar Rivers.

Shugaba Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi SamboHoto: AP

A ranar Asabar ɗin nan ce shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ƙaddamar da Kamfe ɗinsa na yaƙin zaɓen a garin Fatakwal dake jihar Rivers. Jim kaɗan bayan kammala jawabin shugaban ƙasar an sami hatsaniya wadda ta yi sanadiyar jama'a suka firgita. Rahotanni sun ce an tattake mutane da dama a turmutsitsin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 20 yawancinsu mata da ƙananan yara, wasu da dama kuma sun sami raunuka. Turmutsitsin dai ya biyo bayan harbin da 'yan sanda suka yi ne a sama domin tarwatsa cincirindon jama'a waɗanda ke neman shiga dandalin taron. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar Rivers Rita Inoma-Abbey ta ce an kai waɗanda suka sami raunuka zuwa asibiti inda ake duba lafiyarsu. Shugaba Jonathan wanda yace ya kaɗu da hasarar rayukan da aka yi, ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu