Mutane sun mutu a Kamaru a yamutsin bayan zabe
October 27, 2025
Akalla mutane hudu ne rahotanni ke tabbatar da cewa sun rasa rayukansu a Kamaru, a yayin arangama tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan madugun adawar kasar Issa Tchiroma Bakary, wanda ke ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasa, kafin hukumar zabe ta fitar da sakamakon karshe a yau Litinin.
Issa Tchiroma Bakary, wanda ya fafata da shugaban kasa Paul Biya da ya shafe shekara 43 a kan mulki, ya kira magoya bayansa da su fito su yi zanga-zangar lumana, kafin sanar da sakamakon duk da takunkumin kan taron jama'a da gwamnati ta sanya.
Tchiroma na cewa ya samu kashi 54.8 na kuri'un zaben, sai dai masana siyasa da dama na hasashen shugaban mai shekaru 92, Paul Biya, shi ne zai sake lashe wa'adin mulki na takwas a zaben da masu sukar gwamnati ke cewa cike yake da magudi da ma kura-kurai.
A birnin Douala, wanda shi ne mafi girma a Kamaru, gwamnan yankin ya ce masu zanga-zanga sun kai hari kan jami'an ‘yan sanda da wasu ofisoshinsu a unguwanni biyu na birnin.