Mahara sun kashe sojojin Burkina Faso
August 19, 2021Talla
Rahotanni na cewa 'yan ta'adda uku sun mutu a lokacin musanyar wuta da hukumomin tsaro. Shugaban kasar na Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar.
Kasar Burkina Faso na cikin yankin Sahel da ke fama da barazanar kungiyoyi 'yan ta'adda masu alaka da al-Qaeda, sai dai hare-haren sun kara tsanananta ne daga 2015. Tun farko Faransa ta karfafa sojinta a yankin don cimma burin kasashen da ke yankin Sahel na kakkabe ta'addanci. Mutane da dama sun mutu sanadiyyar hare-haren akalla mutane miliyan daya da 200,00 sun yi hijira a cewar Majalisar Dinkin Duniya.