1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Mutane sun mutu a wata majami'a a Najeriya

January 12, 2022

A wani ibtila'in ruftawar majami'a, an samu asarar rayuka ciki har da na yara kanana a yankin kudancin Najeriya. Rugujewar gine-gine dai ba sabon labari ba ne a kasar.

Aachener Friedenspreis 2021 | Treffen mit Gewaltopfern eines Massakers
Hoto: Hartmut Schwarzbach/missio

'Yan sanda a Najeriya, sun tabbatar da mutuwar akalla mutum uku; biyu daga cikin su kananan yara sakamakon ruftawar da wata majami'a ta yi a kudancin kasar.

Ginin ya rufta ne a kansu a wani yanki na garin Asaba babban birnin jihar Delta. Kuma baya ga wadanda suka mutun akwai ma wasu 18 da suka jikkata.

Kafofin watsa labaru na cikin gida, sun ce ginin ya rufta ne a lokacin da ake tsaka da addu'o'i da maraicen ranar Talata.

Matsalar rugujewar gine-gine dai ba sabuwar aba ba ce a Najeriya, kasar da ta fi yawan al'uma a nahiyar Afirka.

Miliyoyin 'yan kasar ne ke rayuwa a gidaje da ma halartar wuraren kamar na ibada da ba su da inganci saboda rashin bin ka'idodijin gine-gine.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW