An sanar da sunayen wadanda suka lashe kyautar Nobel ta bana
October 5, 2020Michael Houghton dan kasar Birtaniya da kuma Hervey J. Alter da Charles M. Rice su ne aka bayyana a ranar Litinin din nan, a matsayin wadanda suka lashe kyautar Nobel ta bana a harkar lafiya. Nasarar da mutanen uku suka samu, ta biyo bayan binciken da suka gudanar da kuma ya yi sanadiyyar gano cutar ciwon hanta mai rukunin C tun a shekarun 1970 zuwa 1980.
Binciken a cewar kwamitin tantance wanda ya lashe kyautar ya taimaka matuka, wajen samun maganin nau'in cutar ta hanta a fadin duniya da ta hallaka mutane da dama, hakan kuma ya kara kyautata kiwon lafiyar al'umma.
Gano nau'in cutar ta hanta mai rukuni C ya biyo bayan wanda aka taba yi na rukunnan A da B wadanda suma ke mummunar illa ga lafiyar bil adama.
Kiyasin hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, WHO, na nuni da cewa kimanin mutane dubu 70 ke kamuwa da cutar a duk shekara inda kuma wasu dubu 400 ke rasa rayukkansu.