Isra'ilawan da Hamas ta saki sun isa Tel-Aviv
October 13, 2025
Rukunin Isra'ilawa na karshe da Hamas ta yi garkuwa da su a zirin Gaza sun isa Isra'ila a Litinin din nan domin musayar su da fursununonin Falasdinu, gabanin taron kasa da kasa da za a yi a Masar kan makomar yankin Falasdinu a rana ta hudu da fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Sanarwar sakin Isra'ilawan 20 da ransu ta janyo murna marar iyaka a dandalin da aka ware domin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a birnin Tel-Aviv, inda dubban jama'a suka taru domin tarbar su.
A gefe guda motocin bas da dama shake da fursunonin Falasdinu sama da 2,000 da Isra'ila ta saki sun isa birnin Ramallah da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da ke karkashin mamaya, inda dubban jama'a suka taru domin yin murna.
Shugaban Amurka Donald Trump da ya isa Tel-Aviv a safiyar Litinin domin shaida lamarin, ya samu tarbar ban girma daga ministocin Isra'ila, inda firaminista Benjamin Netenyahu ya bayyyana shi a matsayin 'babban masoyin Isra'ila'.
Shugaban na Amurka da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sissi za su jagoranci taron kasa da kasa kan makomar zirin Gaza da za gudanar a Charm el-Cheikh, wanda shugabannin kasashen Labarawa da na Musulmi akalla 20 da kuma sakataren MDD za su halarta.