1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mutum 16 sun mutu a harin 'yan bindiga

Ramatu Garba Baba
May 24, 2021

Mutum kimanin 16 aka tabbatar sun mutu a sakamakon wasu hare-haren da 'yan bindiga suka kai a wasu yankuna biyu da ke jihar Filato a yankin tsakiyar Najeriya.

Symbolbild | Nigeria | SWAT
Hoto: AFP/Y. Chiba

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun kai hare haren ne a daren jiya Lahadi, kuma sai yau da rana ne aka sami labarin. Maharan sun kashe mutane takwas a kauyen Dong da ke karamar hukumar Jos ta arewa, yayin da kuma suka hallaka wasu mutane takwas a kauyen Kwi, da ke karamar hukumar Riyom. Tuni wasu suka soma zargin cewa, Fulani ne suka kai hare-haren na ramuwar gaiyya kan al’umomin yankunan biyu.

Kokarin da wakilinmu Abdullahi Maidawa Kurgwi yayi don samun Karin bayani daga hukumomin 'yan sandan yankin kan lamarin ya ci tura, amma kakakin gwamnatin jihar Filato Mista Dang Man Jang, ya ce a guji yada zarge-zarge a game da wadanda ake zargi da hannu a hare-haren, don tuni suka baza jami’an tsaro domin gano maharan. Yanzu haka dai,  an shiga halin zullumi a yankunan da lamarin ya auku, inda kuma aka tura karin jami’an tsaro don tabbatar da doka da oda.