1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLatin Amurka

Mutum 18 sun mutu a hadarin mota a Peru

July 26, 2025

Motar ta bas mai dauke da mutum fiye da 60 ta kife ne a wasu tsaunukan kasar ta Peru a ranar Juma'a.

Akwai wasu daga cikin mutanen da ke jinya a asibiti
Akwai wasu daga cikin mutanen da ke jinya a asibitiHoto: Sebastian Castaneda/REUTERS

Akalla mutum 18 sun mutu bayan wata motar bas ta fasinja ta fadi cikin wani kwari a tsaunukan Andes na kasar Peru a ranar Juma'a, a cewar wani jami'in kiwon lafiya.

Motar, wacce ta kife a kusa da wani kogi, na dauke ne da fiye da mutane 60 da suka taso daga babban birnin kasar Lima zuwa birnin La Merced da ke cikin daji.

Guatemala: Mutane 51 sun mutu a hadarin mota

Mai magana da yawun hukumar lafiyar garin Tarma, wanda ke kimanin kilomita 240 da gabashin Lima ne ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP faruwar hadarin.

Rahotannin farko sun bayyana cewa mutane 15 ne suka mutu, yayin da 30 suka jikkata, amma wasu uku daga cikin wadanda aka kai asibiti sun mutu daga bisani.

Hadarin mota ya halaka mutane sama da 20 a Cote d'Ivore

Kungiyoyin agaji sun samu isa wurin da lamarin ya faru amma har yanzu ba a gano musabbabin hadarin ba.