1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Mutum 46 sun mutu a bikin wankan tsarki na addinin Hindu

September 26, 2024

Hukumomi sun ce mamatan sun bijire wa gargadin shiga koguna yayin da suka cika makil da ruwan sama.

Bikin addinin Hindu na Jitiya Parv Hindu
Bikin addinin Hindu na Jitiya Parv HinduHoto: Sanjay Kanojia/AFP/Getty Images

Hukumomi a gabashin Indiya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 46 sakamakon nutsewa a ruwa yayin wani bikin mabiya addinin Hindu.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce mutanen sun rasu ne a wurare daban-daban a jihar Bihar a yayin da suka je wankan tsarki a kogunan da suka cika kuma suka tumbatsa.

Karin bayani: Gobara ta halaka mutane da dama a Indiya

Daya daga cikin jami'an hukumar da bai sahale a ambaci sunansa ba ya ce mutane sun yi biris da gargadin hukumomi na hadarin da ke tattare da shiga kogunan a yayin da ambaliya ta ke ganiyarta a damunar bana.

Tun a ranar Talata ne aka fara samun labarin nutsewar mutanen a yankuna 15 na jihar ta Bihar a yayin da ake bikin Jitiya Parv Hindu na mabiya addinin Hindu da uwaye ke yi don sama wa  'ya'yansu lafiya da kuma tsarki.

Karin bayani:Mata a Indiya na zanga-zanga kan halaka wata likita

Gwamnatin jihar ta ce za ta biya diyya ga iyalan mamatan 46 da suka gamu da wannan iftila'in yayin wankan tsarkin addininsu.