1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Mutum bakwai sun halaka a hadarin jirgin sama a Mexico

December 23, 2024

Hukumomin Mexico sun fada cewa babu ko mutum daya da ya tsira da ransa daga hadarin da karamin jirgin ya yi.

Hoton wani jirgi da ya yi hadari a Argentina
Hoton wani jirgi da ya yi hadari a ArgentinaHoto: LA NACION/dpa/picture alliance

Rahotanni dake daga yankin Jalisco dake yammacin kasar Mexico sun bayyana cewa akalla mutum bakwai sun halaka bayan faduwar wani karamin jirgi a cikin duhun daji. Jirgin mai lamba 207 ya baro garin La Parota ne na jihar Michoacan makwabciyar garin na Jalisco.

Tsamin dangantaka tsakanin Mexico da Amurka

Hukumomin garin sun fada a shafukan sada zumunta cewa hadarin ya auku ne a wani wuri mai wahalar isa. Tun da farko hukumar kare fararen hula ta garin ta bayyana cewa an kirga gawarwaki bakwai amma ba a iya tantance ko su wanene ba.

Zaman makokin mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi na Iran

Hukumomi sun kara da cewa  suna jiran zuwan masu binciken kwa-kwaf domin daukar gawarwakin kuma suka ce babu wani mutum da ya saura da ba a gani ba.