Mutum fiye da 270 sun mutu a harin Somaliya
October 16, 2017Talla
Sanarwar ministan ta kara da cewa akwai wasu mutane fiye da 300 ke kwance a gadon asibiti sakamakon munmunar harin kunar bakin waken da aka kai a wata unguwa da ke a birnin Mogadishu a ranar Asabar da ta gabata. Gwamnatin Somalia ta daura alhakin harin kan kungiyar al-Shabab duk da cewa babu wata sanarwa daga kungiyar kan harin da ya kasance mafi muni a kasar a yini guda da ya yi sanadiyar rayukan mutane barkatai.
Kasashen duniya da dama sun yi tir da wannan harin a yayin da kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta nemi hadin kan kasashen duniya domin taimakon kasar ta Somaliya a wannan yanayin da ta samu kanta ciki.