1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Mutum miliyan biyar na cikin barazanar yunwa a Sudan - MDD

March 16, 2024

Rikicin da ake gwabzawa a Sudan na kawo cikas ga al'ummar kasar wajen ciyar da kanta da kuma hana isar da kayan agaji ga wadanda ke cikin tsananin bukata.

Mutam miliyan biyar na cikin barazanar yunwa a Sudan - MDD
Mutam miliyan biyar na cikin barazanar yunwa a Sudan - MDDHoto: Mohamed Zakaria//MSF/REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kusan mutane miliyan biyar za su iya fadawa cikin munmunan bala'in yunwa a Sudan nan da watanni masu zuwa sakamakon yakin basasa da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin bangarorin manyan habsosshin sojan kasar da ke hamayya da juna.

Karin bayani: Al'umma na fuskantar matsalar karancin abinci a Sudan

A cikin wata sanarwa, shugaban hukamar jin kai ta MDD Martin Griffiths ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a Sudan, sannan kuma ya bukaci da a samar da hanyoyin kai dauki ga al'ummar wannan kasa da ke cikin halin kunci don kaucewa musu fadawa cikin bala'i mafi muni.

Shugaban hukumar jin kan ya kara da cewa mata da kuma wasu mutane da suka rasa matsugunensu sakamakon yakin na cikin babban hadari, sannan kuma yara kanana kusan 730,000 za su iya fadawa cikin tamowa idan ba akai dauki cikin gaggawa ba.

A daya gefe kuma darektar hukumar lafiya ta duniya WHO da ke Gabashin Afrika Hanan Balkhy ita ma ta yi gargadi game da durkushewar harkokin kiwon lafiya a Sudan musamnan ma a yankin Darfur tun bayan barkewar rikicin kasar a ranar 15 ga wata Afrilun bara.