Mutum na takwas ya kamu da Ebola a Mali
November 25, 2014Talla
Hukumomin kiwon lafiya a ƙasar Mali sun ba da sanarwar cewar an samu mutum na takwas da ya kamu da cutar Ebola a ƙasar. Tun da farko a ranar Asabar da ta gabata ofishin ministan kiwon lafiya na ƙasar ya sanar da cewar an samu ƙarin wani mutumin da ya kamu da cutar.
Gwamnatin ƙasar ta Mali ta ce an killace mutanen a wata cibiya ,ana jinyarsu sannan kuma ta ce ana sa ido a kan wasu mutane 271 da suka yi cuɗanya da waɗanda ake jinyar.