Mutum tara sun rasu a wani hari kan asibitin Sudan
December 14, 2024Wani hari da aka kaddamar kan asibiti a birnin Al-Fashir da ke yammacin Sudan ya halaka mutane tara, tare da raunata 20 ciki har da marasa lafiya da iyalansu a cewar shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce hare-hare kan asibitoci a Sudan sun zama ruwan dare.
Sojojin Sudan sun yi harbi a asibiti
Ya kuma yi kira da a rika kare dukkan marasa lafiya da ma'aikatan kiwon lafiya, da kuma dukkan wuraren jinya.
Tun a watan Afrilun 2023 ne yaki ya fara yayyaga Sudan, inda ake ta fafatawa tsakanin janar-janar guda biyu wato shugaban sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci daukar matakin gaggawa kan yakin Sudan
Tun a watan Mayun wannan shekaran ne Al-Fashir da ya kasance babban birnin Arewacin yankin Darfur, ya fada karkashin sojojin kar-ta-kwana na RSF wadanda suka toshe cinikayya da kuma kayan agaji a yankin.