1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Mutumin da ganinsa ya dawo bayan shekaru 27

Muhammad Bello Dabai /Ahmed Salisu
October 21, 2026

Bayan shafe shekaru 27 cikin duhun rashin gani, idon Abdullahi Abubakar ya bude bayan aikin da aka yi masa. Yanzu yana koyon sabuwar rayuwa daga farko, tare da shirin fara kasuwanci bayan tiyatar da ta sauya masa rayuwa.

Wani makaho a Ivory Coast mai suna Kouadioa-Allaikro
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Idanun Abdullahi Abubakar cike suke da mamaki yayin da yake kallon yadda rayuwa ke gudana a zahiri, a duniyar da tsawon shekaru 27 yana jin hayaniyarta ne kawai a kunnuwansa.

Ya fara fama dalarurar gani tun yana dan shekara uku. Tun daga wannan lokaci, rayuwarsa ta kasance cike da kalubale. Abdullahi ya ce "na kai matsayin da na mika wuya ga rayuwa da makanta. Ban yi tunanin zan sake ganin duniya ba."

Makantar da Abdullahi ya yi fama da ita ta tilasta masa rungumar bara domin samun abin da zai ci da kuma kula da bukatun rayuwa.

Samun sauyin rayuwa bayan tiyata

Bayan wata tiyatar ido da aka yi masa, rayuwarsa ta dauki sabon salo. Ganinsa ya dawo ne a lokacin da ya kusa fidda rai kan yiwuwar sake kallon duniya, sai dai duk da farin cikin dawowar ganin, kalubalen farko da ya fuskanta shi ne koyon yadda ake rayuwa a duniyar da yanzu yake iya gani da idanunsa.

Matshin ya kara da cewa bayan ansarar aikin da aka yi masa duniya ta zame masa sabuwa inda ya ce "komai sabo ne a gare ni. Ina koyon gane mutane, wurare da abubuwan da ke kewaye da ni."

Abdullahi ya bayyana cewa daya daga cikin muhimman abubuwan da yake kokarin koya shi ne yadda zai kare kansa daga hadurra da kuma fahimtar abubuwan da ke faruwa a kusa da shi.

Taimakon makwabta wajen fahimtar sabuwar duniya

A wannan sabon babi na rayuwarsa, makwabta sun taka muhimmiyar rawa wajen taimaka masa sabawa da duniyar gani.

Daya daga cikin makwabtansa, Umar Isah, ya ce suna kokarin taimaka masa ya fahimci wurare da sauye-sauyen da suka faru a garin Wudil tsawon shekarun da ya yi ba tare da gani ba, inda ya ce "yana ta tambayar abubuwa da yawa saboda yana son sanin yadda duniya take a zahiri''.

Kokarin neman na kai

Sannu a hankali, Abdullahi na kara fahimtar muhallinsa da sabuwar rayuwar da ya tsinci kansa a ciki kuma ya fara shirye-shiryen dogaro da kai ta hanyar kasuwanci.

Daya daga cikin abubuwan da yake mayar da hankali a kai shi ne koyon bambance takardun kudi, domin ya samu damar gudanar da harkokinsa cikin sauki.

Bayan samun tallafin jari daga wasu 'yan siyasa a yankinsa, ya zabi shiga kasuwancin dabbobi, wanda yake fatan zai zama sabon tushen samun kudin shiga. "Ina son in yi kasuwanci na kaina. Burina shi ne in daina dogaro da bara kuma in gina rayuwa mafi kyau."

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani