1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutumin Faransa zai ja ragamar mulki a Mali

August 16, 2013

Tun ba a sanar da sakamakon zaben a hukumance ba shugaban Faransa Francois Hollande ya taya Ibrahim Boubacar Keita murnar lashe zaben da cewa nasara ce ga demokradiyya.

ARCHIV - Ex-Ministerpräsident von Mali Ibrahim Boubacar Keita spricht zu seinen Unterstützern in seinem Hauptquartier in Bamako, Mali am 04.05.2013. Am 11.08.2013 findet die Stichwahl zwischen Boubacar Keïta und Ex-Finanzminister Cissé statt. Foto: EPA/TANYA BINDRA +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Mali. A sharhin da ta rubuta mai taken sabon babi da tsoffin fuskoki jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi:

"Mali ta samu sabon shugaban kasa wanda zai ja ragamar aikin ceto kasar daga rikice-rikicen da take fama da su. Ibrahim Boukacar Keita wanda 'yan kasar Mali ke kiransa IBK, ya lashe zaben shugabancin kasar bayan yayi takara sau uku. Ko shakka babu zaben Ibrahim Boubacar Keita a matsayin shugaban Mali tamkar wani wakilin tsohuwar gamnatin kasar aka zaba. Sai dai idan aka kwatanta shi da sauran 'yan siyasar kasar ana iya cewa mutum ne mai kamanta gaskiya. Ko da yake a lokacin da ya rike mukamin Firaminista daga shekarar 1999 zuwa 2000, ya azurta kansa, amma ga al'ummar kasar, bai kai abokin hamaiyarsa Souma'ila Cisse dake zaman tsohon ministan kudin kasar, wasashe dukiyar talakawa ba."

Francois Hollande lokacin wata ziyara a MaliHoto: Pascal Guyot/AFP/Getty Images

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a lokacin da take sharhi kan kasar ta Mali cewa ta yi mutumin da Faransa ke goya wa baya zai ja ragamar shugabancin Mali, sannan sai ta ci gaba kamar haka:

Zaben Mali nasara ga demokradiyya

"Masu sa ido a zabe na kasashen yamma sun yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar Mali, wadda kawo yanzu ta yi ta fama da tashe-tashen hankulan masu kaifin kishin addini. Tun ba a sanar da sakamakon zaben a hukumance ba shugaban Faransa Francois Hollande ya taya Ibrahim Boubacar Keita dake zama mutumin da Faransa ke marawa baya, murnar lashe zaben da cewa nasara ce ga demokradiyya kuma Faransa za ta dafa masa baya. Shi dai Keita a Faransa yayi karatun jami'a har ma kuma ya koyar. Wani kamfanin hulda da jama'a na Faransa ya jagoranci yakin neman zabensa."

Ayyukan 'yan bindiga a arewacin Najeriya

Ayyukan 'yan bindiga ya ki ci ya ki cinyewa a NajeriyaHoto: AMINU ABUBAKAR/AFP/Getty Images

Mutane da yawa sun rasu a wani hari da aka kan kan masallaci a Najeriya, inji jaridar Frankfurter Allegemeine Zeitung tana mai sharhi a kan harin da jami'an tsaron Najeriya suka dora laifinsa a kan kungiyar nan da ake wa lakabi da Boko Haram, sannan sai ta ce:

"Jaridun Najeriya dai sun ce wannan harin na da alaka da karuwar kungiyoyin matasa masu kare kai daga 'yan Boko Haram, domin harin yayi kama da wanda aka kai a kan 'ya'yan kungiyoyin kare kai a jihar Borno a tsakiyar watan Yuni da ya gabata inda aka kashe mutane 25. A cikin watannin bayan nan dai an horas da matasa da yawa dubarun yadda za su kare kauyukansu daga hare-haren masu kishin addini tare da rage kaifin mayakan Boko Haram. Sojojin Najeriya ke ba wa wadannan kungiyoyin kare kai makamai. Sai dai duk da tsauraran matakan tsaro da aka dauka da kuma dokar ta-baci da aka kafa a jihohin Borno, Yobe da Adamawa cikin watan Mayu, babu wani lahani na a zo a gani da aka yi wa kungiyar ta Boko Haram, domin har yanzu tana iya kai hari a inda ta so da kuma lokacin da ta so ba tare da shakkan kowa ba."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman