1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mutuwar bakin haure a yunkurin shiga Spain

Suleiman Babayo AMA
December 29, 2025

Bakin haure fiye da 3,000 da suka fito daga nahiyar Afirka suka hakala a kokarin shiga kasar Spain a wannan shekara ta 2025, lamarin da ke nuni da ci gaba da samun neman shiga kasashen Turai ta barauniyar hanya.

Bakin haure masu neman shiga Spain daga Afirka
Bakin haure masu neman shiga Spain daga AfirkaHoto: Europa Press Canarias/imago images

Fiye da bakin haure 3,000 suka hakala a kokarin shiga kasar Spain a wannan shekara ta 2025 da ke karewa. Wani rahoton kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta Spain, ta fitar a wannan Litinin ya nunar da cewa alkaluman sun ragu daga na shekarar da ta gabata ta 2024. Fiye da bakin hauren 10,000 suka mutu ko kuma suka bace a shekara ta 2024 a kokarin shiga kasar ta Spain.

Adadin bakin hauren ya ragu

Bakin haure masu neman shiga Spain daga AfirkaHoto: Europa Press Canarias/imago images

Bakin haure da suka halaka masu neman shiga kasar ta Spain sun fito ne daga nahiyar Afirka, galibi daga kasashen Aljeriya da Somaliya da Sudan da Sudan ta Kudu.

Sannan ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta Spain ta bayyana cewa fiye da bakin haure 35,000 suka shida kasar daga farkon shekarar da muke ciki ta 2025, zuwa wannan wata na Disamba, abin da ke nuna raguwa da kaso 40 cikin 100 na wadanda suka shiga kasar, idan aka kwakwanta ta shekarar da ta gabata ta 2024.